Ku Ƙwato Najeriya daga hannun Miyagu, Obi ga Matasa
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya kalubalanci matasan Najeriya da su kwato Najeriya daga hannun gurbatattun shugabanni su samar da kasar da suke so kuma da za su yi alfahari da ita.
Obi ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a wani taron matasa na kasa da kasa a Enugu mai taken; ‘Yin amfani da lokaci don tsara makomar gaba’.
KARANTA WANNAN LABARIN: Najeriya Ba Ta Bukatar Dan Takarar LP, Kirar Sunan Shi Ma Abun Kunya Ne—- Tinubu
Obi ya ce yana samun kwarin guiwa a wajen zaben da kuma abubuwan da matasan suka nuna ya zuwa yanzu a tunkarar babban zabe na 2023, ya kara da cewa canjin da Najeriya ke bukata a zahiri ya dogara ga matasa.
Dan takarar jam’iyyar LP ya kara da cewa hare-haren da aka kai masa shaida ne da ke nuna cewa yana adawa da mutanen da ke nufin cutar da Najeriya.
Da yake ambaton wani babban dan gwagwarmayar zamantakewar jama’a na Amurka, Martin Luther King Jr, Obi ya ce, “Karkin sararin samaniya yana da tsayi, amma yana karkata zuwa ga adalci.”
Ya ci gaba da cewa, “Muna samun kwarin guiwa, musamman irin kishi da jajircewar da matasanmu suke yi, da kuma jajircewarsu wajen kwato kasarsu, su gina wa kansu irin al’ummar da suke so.
A wani labarin kuma: A Karon Farko, Wani Ɗan Zamfara Ya Zama Babban Lauya a Najeriya
Masu fada a ji a jihar da ke cikin farin ciki sun yi ikirarin cewa tun da aka kafa jihar a shekarar 1996, ba ta da wani babban lauyan Najeriya mai muƙamin (SAN).
Da yake magana DAILY POST a garin Gusau, Andi Haliru, tsohon mai ba gwamnan jihar na farko shawara kan wayar da kan jama’a, Ahmed Sani Yarima, ya ce al’ummar jihar suna alfahari da kasancewar su Sani Abdul Aziz Mohammed.