Shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya umurci magoya bayan jam’iyyar da su adana makamai domin fuskantar zaben 2023.
Shugaban jam’iyyar ya ce za a farwa duk wanda ya yi yunkurin aringizon zabe da wadannan makamai da za a tara.
Ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su ci kaniyar duk wani mutum ko kungiya da za su yi yunkurin murdiya da aringizon kuri’u a babban zaben 2023 idan ya zo.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke jawabi ga dandazon jama’a a yayin rantsar da sabbin shuwagabannin kananan hukumomi 44 na jihar Kano, da ya gudana a ranar Juma’a a Kano.
Bayan yin holen irin makaman da suke dauke da su a lokacin, yayin tabbatar da taken jam’iyyar APC, shugaban jam’iyyar sai kuma ya umurci matasan da su ajiye makaman, yana mai cewa, “za mu fadi maku lokacin da za ku yi amfani da wadannan makamai.”