Tsohon Sanata Mai Wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya buƙaci Gwamanati data ayyana ƴan bindiga a matsayin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, tunda sun kasa gano cewa ƴan ta’adda ne.
Sani ya bayyana haka a shafin sa na Twitter, a lokacin da yake nuna rashin jindaɗin sa akan kisan Musulmai da Kiristoci a gidajen su na ibada.
Yace rubuta kamar haka “ƴan bindiga sun kashe musulmai a masallacin su a Jahar Niger da Katsina, sun kashe kiristoci a cocinan su a Jahar Kaduna, idan Gwamnati bata son ayyana su a matsayin ƴan ta’adda, to ta ayyana su a matsayin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaɓa ta a cikin Shuwagabannin Jam’iyyar PDP zai ceto Najeriya daga APC — Cewar Anyanwu
Sanata Shehu Sani ya bayyana kulle layukan sadarwa a matsayin abinda bai amfanar da komai ba, wanda anyi shine domin a magance ƴan bindiga daɗi.
Yace “harin da ƴan bindiga suka kai a cocin Baptist ta Kakau Daji, Jahar Kaduna, kashe wasu masu ibada, da sace wasu abin baƙin ciki ne. Kulle layukan Sadarwa a Yankin Arewa bai amfanar da komai ba.