Kwamishiniyar bunkasa sana’o’in ‘ya’ya mata ta jihar Delta, Misis Nkechi Enumah-Chukura, ta yi kira ga ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su bayar da gudumawarsu don farfado da rayuwar wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a fadin kasar nan. Kamar yadda Punch Ta ruwaito.
Enumah-Chukura, wadda ita ce shugabar shiyyar Kudu-maso-Kudu ta kungiyar goyon bayan Atiku, ta bayyana haka ne a lokacin da ita da sauran ‘ya’yan kungiyar ta suka ziyarci wasu al’ummomin da lamarin ya shafa a karamar hukumar Ndokwa-Gabas inda ta raba kayayyakin abinci da tsabar kudi amatsayin gudummawa ga wadanda abin ya shafa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Kama Mataimakin Kakakin Majalissar Dokokin Imo Tare Da Tsare Shi
Nkechi, ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na kungiyar goyon bayan Atiku, Victor Moses, ya fitar, inda ta ziyarci wasu al’ummomi bakwai da suka hada da Akarai-Obodo, Umuti, Iyowu, Okpokrika da Afiankwo, inda ta bayar da gudummawar katun 100 na taliya, buhu 30 mai dauyin kilogram 50 na wake, buhunan albasa guda hudu da wasu kudi.
Sanarwar ta nakalto ta na cewa, “Duk da muna matukar godiya ga gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, mun yi kira ga ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su kai dauki ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa domin gwamnati na bukatar mutane masu zaman kansu da kuma kungiyoyi masu zaman kansu su da su kawo dauki.”
A wani labarin kuma, Najeriya Ba Ta Bukatar Dan Takarar LP, Kirar Sunan Shi Ma Abun Kunya Ne—- Tinubu
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya ce zai zama abin kunya idan ya ambaci sunan takwaransa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi.
Tinubu ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi a wani gangami a Gbaramatu na, jihar Delta a ranar Juma’a