Gwamnan Jahar Katsina Aminu Bello Masari ya kalubalanci Jahohin Lagos da Rivers akan matsayar su, na karbar ragamar amsar kudaden haraji a Jahohin su.
Masari yace dukkanin Jahohin Lagos da Rivers baza su samu makudan kudaden haraji da ake basu ba, idan ba tare da gudunmuwar wasu Jahohin ba.
Gwamnan ya bayyana matsayar dukkanin Jahohin guda biyu da suka hada da; Lagos da Rivers a matsayin wasa, yana mai cewa dukkanin su, sun dogara ne da yawan al’ummar wasu Jahohin domin bunkasa tattalin arzikin su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 20 sun kubuta bayan Jirgin yakin Sojin Saman Najeriya ya razanar da barayin daji a Katsina
“Wace ce Lagos idan babu sauran sassan Nigeria? Kasuwar da Lagos ke takama da’ita ya dogara ne da kaso mai yawa na kasar. Jamhuriyar Benin nada tashohin ruwa, Togo nada su, suna da yawan mutanen da zasu kula dasu? Ba tare damu ba, muda muke samar masu da bukatun su, mi Lagos zata zama?
“Kudaden haraji na VAT, ya taimake su damu. Muna bada kaso Mai yawa na kasuwancin su, ba tare da sauran jahohi ba, micece Lagos da Port Harcourt?
“Duk Jahar da take tunanin zata iya rayuwa ita kadai to tana wasa ne. Muke bada abubuwan da suka maida Lagos yadda take a yanzu,” Masari ya shaidawa majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta Daily Trust.
Duka Jahohin Lagos da Rivers sun yi wani yunkuri na karbe ragamar cigaba da karbar kudaden haraji, daga Hukumar tattara kudaden haraji ta Kasa wato-FIRS.
Amma lamarin a halin yanzu yana a gaban kotun koli ta Kasa.
Haka zalika, Gwamnonin Kudu sun cire hannun su akan goyan bayan kudirin Jahohin Lagos da Rivers.