Darakta-Janar na Hukumar yi wa kasa hidima (NYSC) na 19, Birgediya-Janar Mohammed Kaku Fadah, ya soma aiki.
Da yake magana a ranar Laraba yayin bikin mika mulki da karbar ragamar mulki da aka gudanar a Abuja, ya ce zai ci gaba da rike abin da ya gada daga magabacinsa.
“DG mai barin gado na NYSC ya bar mini wani babban aiki a gabana kuma ina fatan in yi aiki tukuru don dacewa da shi. Duk ayyukan da ke gudana, zan tabbatar da an kammala su. Duk abin da na gada za a kiyaye,” inji shi.
Fadah ya bukaci ma’aikatan Hukumar da kada su rika gudanar da ayyukan da ba su dace ba kamar gulma da sauransu, su hada kai da shi domin kai wannan shirin na yiwa kasa hidima zuwa ga wani matsayi.
Babban daraktan NYSC mai barin gado Manjo-Janar Ibrahim Shuaibu ya bukaci ma’aikatan da su bada goyon bayansu ga magajinsa.
A wani labarin Kuma na daban.
Idan Aka Zabe Ni Shugaban Kasa, Yan bindiga Sai Sun Rasa Mafaka——-Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasar nan, Yan bindiga bazasu Kara samun maboya ba.
Yayin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar PDP a Katsina a ranar Laraba, Atiku ya ce sakacin shugabanni ne ya ba masu laifi damai ci gaba danumfashi.
Ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben shekarar 2023 zai tabbatar da cewa babu wani mai laifi da zai tayar da ta’addanci a kan ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba kuma masu son zaman lafiya ba tare da komowa ba.
“Muna tahowa Katsina tare da tsohon gwamnanku Ibrahim Shema a cikin jirgi na na kashin Kai, kuma babu inda ba mu iya gani a kasa. Ina abin da ake cewa dajin da masu laifi suke boye da ba za a kai gare su ba?.
“Ina tabbatar muku da cewa idan kuka ba ni goyon bayanku na zama shugaban kasa a 2023, batun rashin tsaro zai kasance cikin manyan abubuwan da muka sa a gaba, kuma na yi alkawarin dawo da zaman lafiya a Katsina da kasa baki daya.
Daga nan Atiku ya bayyana sauran bangarorin da zai mayar da hankali a kai idan aka ba shi dama, da suka hada da hadin kan kasa, tattalin arziki, ilimi, da mika mulki ga jihohi.
Ya godewa wakilan Katsina bisa abin da ya kira goyon bayansu a shekarar 2019 a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas, inda ya ce sun taimaka masa wajen ganin ya zarce sauran masu son daga tutar jam’iyyar.
A cikin tawagarsa akwai Cif Raymond Dokpesi da Sanata Baraka Sani da Sanata Abdul Ningi da Alhaji Adamu Maina Waziri da tsohon sakataren PDP na kasa Umar Tsauni.