Ku baiwa Mata Takarar Kujerun Mataimakin Gwamna — CSO tayi kira ga Jam’iyyun siyasa
Ƙungiyar Fararen Hula mai Suna Brain Builders Youth Development Initiative ta shawarci Jam’iyyun siyasa dasu yi wata doka da zata baiwa Mata damar zama Ƴan Takarar Mataimakan Gwamnoni a Jahohi 36, domin inganta shigowar nata a harkokin Siyasa a Ƙasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Korarran Hadimin Gwamna Ganduje Ya Bayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Gwamnan Kano
Ƙungiyar ta bada wannan shawarar ne a Ilori, Jahar Kwara, a lokacin data ƙaddamar da wani shiri na ta data tsara domin samo wa mata kujeru da yawa a ɓangaren Zartaswa dana Majalisu a Ƙasar.
A cewar Ƙungiyar, Ƙididdiga ta nuna cewa yanayin yanda aka baiwa Mata kujeru a Siyasa a Najeriya abun babu daɗin ji a cikin lamarin.
Ta ƙara dacewa, “Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa a wani rahoto nata, tace kashi 13 daga cikin ƴan takara 24,353 da suka yi takara a Kujeru da dama a Shekarar 2019 suka zama Mata.
Dayake jawabi a lokacin da yake ƙaddamar da shirin, Shugaban Ƙungiyar Tolulope Gbenro ya jaddada buƙatar ƙirƙira tare da baiwa Mata dama ƴan siyasa a manyan kujeru domin samun cigaba.