Mohammed Abacha ya bukaci wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta tilasta wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta dakatar da sauya sunansa a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano.
Abacha, ya kuma kalubalanci batun da Jafar Sani Bello, wanda ya zo na biyu a zaben fidda gwani, na cewa shi ba dan jam’iyyar ba ne, domin shi ne aka tantance a matsayin dan takarar na jam’iyyar PDP.
Asalin sammacin da lauyoyinsa, J.Y. Musa (SAN) da Reuben Atabo (SAN), suka shigar sun hada da; hukumar zabe mai zaman kanta (INEC); Sadiq Aminu Wali na jam’iyyar PDP; da Alhaji Shehu Wada Sagagi a matsayin wadanda ake tuhuma.
Abacha ya kara da cewa shi ne ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka gudanar a ranar 25 ga watan Mayu kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta turo jami’anta da suka sanya ido yayin zaben, inda ya samu kuri’u 736, Ja’afar Sani Bello kuma ya samu kuri’u 710 kafin a sauya sunansa da na Wali.
Yakara da cewa, Yana son kotu ta hana jam’iyyar PDP da shugabanta na jihar Sagagi gabatar da Wali a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.
Kazalika Ya ci gaba da cewa INEC ta hana ta “gane tare da wallafa sunan wanda ake kara na 2 (Wali) a matsayin dan takarar gwamna wanda ya kare na 3 (PDP).
Daga karshe dai, An dage sauraron karar har zuwa ranar 12 ga watan Satumba domin ci gaba da sauraren karar.