Daga: Abbas Yakubu Yaura
Wani tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Chibudum Nwuche, ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta gaggauta shiga tsakani domin dakile tabarbarewar da al’ummar kasar ke fuskanta a halin yanzu.
Nwuche, a wata sanarwa da ya fitar jiya Laraba, ya ce a halin yanzu kasar na cikin halin rashin tsaro da ba a taba yin irinsa ba tare da ci gaba da kashe-kashe da sace ‘yan kasar da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga suke yi.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/shugaba-buhari-ya-kira-taron-tsaro-na-gaggawa-yayin-da-sanatoci-suka-yi-barazanar-tsige-shi/
Ya kuma bukaci ‘yan majalisar tarayya da su mayar da hankalinsu kan lamarin tsaro, su kuma kawo wadanda suka yi kasa a gwiwa.
Ya ce rayuwar al’ummar kasar na cikin hatsari ne ga ‘yan kasa ba za su iya tafiya ba, Naira ta yi kasa a gwiwa a kan Dalar Amurka, da tabarbarewar tattalin arziki, rashin aikin yi da matasa ke fama da su, da wahalar da ‘yan Nijeriya da ba za a iya misaltawa ba a cikin halin da ake ciki.
Ya ce, “Kimar kasa da kasa na kasarmu ya kai ga koma baya saboda matsalolin tattalin arzikinmu da rashin shugabanci ya haifar.”
A Wani Labarin Kuma Kwanturola Hukumar Kula da Gidajen Yari na jihar Kogi, David Igbago, ya bayar da umarnin cafke wani jami’in Hukumar nan take bisa laifin bacewar bindigogi biyu da wasu alburusai na Hukumar.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Hukumar Gidan Yarin jihar, DCS Nihi Sesan, wanda aka rabawa Manema Labarai a Abuja ranar Laraba, bai ambaci sunan wanda ake zargin ba.
Sai dai ta ce an sanya jami’in ne a tsarin Shuwagabanci kafin a miƙa shi ga Hukumar tsaro da ta dace domin ci gaba da yi masa bincike.
Sanarwar ta ce an gano abubuwan da suka ɓace ne a yayin gudanar da binciken makamai da alburusai da aka saba yi duk wata a cikin rumbun ajiyar makamai na Hukumar.
Igbago ya sha alwashin tabbatar da cewa ba a bar wani abu ba wajen bankado al’amuran da suka dabaibaye wannan aika-aika tare da gurfanar da masu laifi a gaban kuliya.
Ya kuma bai wa jama’a tabbacin da ya ke da shi na tabbatar da tsaro a jihar Kogi baki daya da ma cibiyoyin kula da lafiya a jihar.