Shugaban hafsan sojin kasa (COAS), Laftanar Janar Farouk Yahaya, ya bukaci sojojin da ke yaki da masu tayar da kayar baya su kasance cikin shiri da kuma ci gaba da gudanar da rayuwar sadaukarwa domin shawo kan matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar.
Janar Farouk, wanda shugaban tsare-tsare na rundunar, Manjo-Janar Andrew Omozoje, ya wakilce shi a ranar Asabar din da ta gabata yayin wani liyafar cin abincin rana ta hadin gwiwa da aka shirya wa sojoji a Maiduguri.
Ya kuma kara jaddada aniyarsa na inganta ayyukan jin dadin sojoji da iyalansu, musamman wadanda ke bukatar agajin gaggawa na kiwon lafiya, yana mai tabbatar da cewa za a ba su kulawa, a cikin gida da waje idan akwai bukatar hakan.
“Sallah ya ba mu dama ta musamman don yin tunani da kuma yi addu’a don neman yardar Allah Madaukakin Sarki Ya karya duk masu zagi da kuma kawo mana dawwamammen zaman lafiya a kasarmu. Ina roƙon ku da ku ci gaba da kasancewa da ƙwararrun ƙasar nan, da kishin ƙasa kuma ku kasance masu tsayuwa a cikin ruhi a duk lokacin da kuke bakin ayyukanku.
“Ina da sha’awar samar da ingantaccen aikin a fannin kiwon lafiya ga waɗanda suka sami rauni a fagen daga a cikin gida da waje, musamman don ba da tallafin ƙarfafawa don samun damar shiga cikin al’umma. Jindadin zai taimaka musu su shawo kan matsalolin da suka faru bayan rauni, ”in ji shi.
Anashi bangaren da yake jawabi Shugaban tsare-tsare na rundunar sojin saman Najeriya Air Vice Marshal Charles Ohwo, ya godewa dakarun bisa sadaukarwar da suka yi, ya kuma yi alkawarin cewa sojojin ba za su huta ba har sai an kawo karshen rashin tsaro fadin Najeriya.
A wani labarin kuma na daban.
Ina Da Kwarin Gwuiwar Buhari Zai Dawo Da Zaman Lafiya A Nijeriya Kafin Ya Bar Ofis—-Malami
Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya ce kafin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kare a shekara mai zuwa, kasar za ta dawo da martabar da ta ke a baya, inda za a samu zaman lafiya.
Ya kara da cewa shugaba Buhari yana aiki ba dare ba rana domin ganin an samar da dukkan hanyoyin da za a bi wajen mika mulki ba kawai a shekara mai zuwa ba, har ma da tabbatar da ganin an kawo karshen kalubalen da ake fama da shi na rashin tsaro a kasar nan.
Malami ya bayyana haka ne a ranar Asabar a lokacin da yake taya al’ummar Musulmi murnar bikin Sallar Idi na bana a Birnin Kebbi.
“Ina so in tabbatar muku cewa gwamnatin Buhari za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaron kasar nan. Ina addu’ar Allah ya amsa addu’o’inmu domin a samu dawwamammen zaman lafiya a jihar Kebbi da kasa baki daya, tare da samun canjin siyasa cikin kwanciyar hankali a farkon shekara mai zuwa,” inji shi.