Ku daina Saida Ƙuri’un ku, mu maida hankali akan gaba — Inji Don Jazzy
Fitaccen Attajirin Mawaƙi Don Jazzy yayi kira ga ƴan Najeriya dasu daina Saida Ƙuri’ar su, yana mai cewa ya fahimci cewa babu sauƙi akan batun daina saida kuri’a, domin tuni saida kuri’a ya “lalata harkokin zaɓe.”
Yana mai bayyana saida kuri’a a matsayin Babbar Annoba, Mawakin a shafin sa na Twitter ya shaidawa mabiyan sa dasu maida hankali akan rayuwar gaba, idan suka zaɓi Shugaban daya dace.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotun ECOWAS ta yanke hukunci, tace Kulle Twitter ya saɓawa Doka, ta gargaɗi Najeriya kan sake aikata wa
“Nasan cewa daina saida kuri’a daya lalata mana zukata abune mai wahala a daina. Ina kira ga ƴan Najeriya dasu maida hankali su zaɓi mutanen da suka dace, duk da yunƙurin da za’a yi masu na saida kuri’ar su,” Inji shi.
Don Jazzy ya Shawarci mabiyan sa dasu daina zama “makamin lalata yanayin zaɓe.”
“Dole mu wayar da kan mu domin ma guji saida kuri’a tare da gudun duk wani abu da za’a yi amfani damu domin lalata yanayin zaɓe. Dole mutane su yi abinda yake haƙƙin su ba tare fin ƙarfi, ko cin zarafi,” Inji shi.