A jiya ne Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya ziyarci wasu gonakin shinkafa da alkama a Birnin Kebbi da Makera domin ganin yadda manoma ke gudanar da harkokin noman rani a halin yanzu.
A yayin ziyarar, Bagudu ya tattauna da manoma maza da mata a yankin fadama da ke daura da yankin Birnin Kebbi/Makera, inda ya sanar da su shirin gwamnatin jihar na tallafa musu domin bunkasa noman su.
Ya shawarci manoman da su dauki dabarun noman zamani domin samun amfanin gona Mai yawa.
Sai dai ya bukaci manoman da su tabbatar sun hada da Kai da ma’aikatan aikin gona kafin su fara ayyukan su na bana..
Anasu bangaren Manoman, sun godewa Gwamnan bisa goyon bayan da yake ba su, tare da neman taimakon da ya dace domin magance matsalar zai-zayar kasa a wasu sassan Fadama da kuma samar da karin taki Mai Ingancin.
A wani labarin Kuma na daban
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Iseyin/Itesiwaju/Kajola/Iwajowa a majalisar tarayya, Shina Peller, ya yi kira ga matasa da sauran ‘yan Najeriya da su yi hattara da ‘yan siyasar da za su yi amfani da su wajen cika burinsu na siyasa a kasar.
Dan majalisar daga jihar Oyo ya bayyana haka ne a sakonsa na Easter da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Kola Popoola ya rabawa wakilinmu ranar Litinin.
Ya bayyana Yesu Kiristi a matsayin mutum ne wanda koyarwarsa da kyawawan halayensa ke wakiltar zaman lafiya da kowace al’umma har da Najeriya ke bukatar ci gaba.
Dan majalisar tarayya ya lissafa dabi’un Yesu Kiristi da suka hada da zaman lafiya, tawali’u, juriya, sadaka, hakuri, gaskiya, jajircewa, tausayi, karimci, aminci, amana, adalci, kamun kai, gafara, kauna da mutunta wasu, wadanda ya ce duka su ne halayen da ake buƙata don al’umma don samun ci gaba.
Ya hori Kiristoci da Musulmai da su yi koyi da kyawawan halaye na Kristi don samun damar magance mafi yawan matsalolin da kasar ke fuskanta.
Ya ce, “Don haka yayin da muke gudanar da bukukuwan Easter, ina rokon mu duka mu yada soyayya, wa’azin zaman lafiya da watsar da alheri da jin dadi a ko’ina a kewayen mu.
“Mu kasance masu hakuri da juna ba tare da la’akari da bambancin addini, kabilanci da siyasa ba. Sama da duka, mu kasance masu adalci a cikin maganganunmu da mu’amalarmu da juna.
“Abu mai mahimmanci, kamar yadda babban zaben 2023 ya nuna, ba za mu bar wani dan siyasa ya yi amfani da mu ba da gangan ko kuma ya yi amfani da mu wajen cika burinsa na siyasa ko sha’awarsa wajen cutar da muradun kasarmu baki daya.
“Kada mu yarda a yi amfani da kanmu a matsayin kayan aikin rarrabuwa da tashin hankali. Lokaci ya yi da zamu yi watsi da ubangida na siyasa amma mu mai da hankali kan gina cibiyoyi masu ƙarfi waɗanda tsara waɗanda ba a haifa ba za su yi alfahari da su. Har yanzu, Barka da Easter zuwa gare mu duka.”