Wata Amaka ciki da farinciki ta bayyana wasu kyawawan hotunan shagalin aurenta kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
A cewar Amaka, ‘yan matan da suka san ba su da samari su dinga kula sakonnin mazan da ke turo musu, inda tace akwai mazajen aure da dama a Facebook.
KU KARANTA: FG ta amince da fara ba ma’aikata maza hutun haihuwa
Ta nuna farincikinta kan yadda ta samu mijin aure a Facebook. Kamar yadda ta wallafa:
“Akwai mazan aure dayawa a Facebook, ku dinga amsa sakonninsu. Na hadu da nawa mijin a Facebook, na hadu da abokin rayuwata.
“Ku taimaka ku taya ni murna. Na fita daga jerin ‘yan mata.”
Saboda diri na maza ke baro garuruwa don cincirindon siyan abinci na, Budurwa
A wallafar ta ci mazan Ghana na kamo hanya daga nesa musamman don siyan abincinta.
Ta shaida yadda a baya take sayar da biredi wanda daga baya ta koma sana’ar abinci.
Ta ce asali kanwar babarta ce ke sana’ar, bayan ganin ta tsufa ne yasa ta amshi sana’ar hannu bibbiyu.