Babban hafsin Sojin kasar nan Tukur Yusuf Burutai ya bukaci Jami’ai dake bakin daga su fada mishi Matsalolin da suke fuskanta a bakin daga.
A wata ziyara da ya kai Jihar Borno dake Arewa maso gabashin kasar nan inda ake fama da kalubalen BokoHaram, Burutai yayi wani zama da Jami’an dake bakin daga inda ya bukace su da su bayyana mishi abubuwan da suke ci musu tuwo a kwarya.
Yace mafi yawan ku kun taso ne daga waje mai nisan gaske zuwa nan bakin daga to ya zama wajibi mu tsare muku hakkokin ku, don mu cimma kalubalen dake gaban mu.
Da yawan ku baza ku bai zama lallai ku iya tunkarar Kwamandojin ku da wata matsalar dake damun ku ba, to yau ranar bude ciki ce ku fada mun kan ku tsaye kuma nayi muku alkawari babu wanda zan bari ya hukunta ku a kan haka.
Burutai, yace kun sani cewar dukkan sauye sauyen gyare gyare mun yi muku kuna samun alawus alawus din ku yadda ya kamata to amma baza a rasa wasu yan matsaloli ba.
Daga bisani ya Umarci Yan Jaridu su fice daga harabar don su jaruman bakin dagar su bayyana matsalolin dake gaban su.