Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma ya ja hankalin jami’an tsaro da kada au ragar ma ko wani dan fashin daji, domin tsaron al’umma ya fi na mutum guda.
Kazalika Uzodinma ya ce muddin jami’an tsaron suka yi rikon sakainar kashi wa harkar tsaro to lallai yan fashin dajin za su ga bayansu.
Gwamna Uzodinma yana wannan jan hankali ne a ranar talata yayin da ya kai ziyarar ta’aziya ga Shelkwatar rundunar yan sanda ta birnin Owerri.
“Ku ne kaɗai doka ta sahale muku ju mallaki bindiga, amma kun bar wadansu da ba sun san menene doka ba kuma a ce suna cin karensu babu babbaka”
“Ku Murkushe su fa tun kafin su gama da ku” cewar Uzodinma.
Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta samar sa inshora ga kowani jami’an tsaro a jihar da zummar kawo karshen matsalolin dake addabar Jihar.