inec

Ku Gudanar Da Sahihin Zabe A Kogi Da Bayelsa- Sakon PDP Ga INEC

Jam’iyyar PDP ta shawarci hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC da ta yi amfani da zaben gwamnan Kogi da na Bayelsa domin ta nuna kanta a matsayin wadanda za su gudanar da sahihin zabe ba tare da murguda zaben ba.

Sakataren yada labaran jam’iyyar PDP din na kasa, Kola Ologbondiyan shi ne ya yi wannan kiran a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin A Abuja. Ologbondiyan ya yi wannnan kiran ne a yayin da INEC din ta tura Kwamishinonin zaben na kasa da na jihohi zuwa jihohin Kogi da Bayelsa.

PDP din ta ce jam’iyyarsu tuni take da cikakken bayani akan dukkanin Kwamishinonin zaben da INEC ta tura jihohin. PDP din ta ce daga cikin bayanan da suka samu, wadansu daga cikin Kwamishinonin zaben da aka tura ba su da wani rahoto na almundahana da murguda zabe, a yayin da wasu a cewar PDP din suke da alamomin tambaya dangane da ayyukan zabe da aka ba su a baya.

PDP ta gargadi shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da tura wadanda suke da alamar tambaya wuraren zaben, wanda suka ce; hakan zai sanya wa zaben alamar tambaya. Ya shawarci INEC da ta bai wa al’umma abin da suka zaba a yayin zaben.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *