Jagoran adawa a kasar Kenya Raila Odinga yayi kira ga Hukumar Zaben kasar Mai zamar Kanta da ta tabbatar da cewa an gudar da zaben kasar cikin gaskiya da adalci
Mr Odinga ya shaidawa kafar yadda labaria ta BBC cewa, ya na daya daga cikin wadanda magudin Zabe ya shafa a baya, Wanda a yanzu yake fatan ganin an Sami sauyi.
.
Ya Kara da cewa, rikicin da Ake samu bayan Zabe, sakamakon ne na rashin Adalci a yayin Shirye-Shiryen gudanar da zaben.
Kazalika Mr Odinga ya yi kira ga abokin hamaiyarsa Kuma Mataimakin shugaban kasar ta Kenya William Ruto da ya kula yayin da yake kokarin Samar da wata cibiya.