Darakta Janar na Hukumar Kula da Matasa masu yiwa kasa hidima, Birgediya-Janar Shuaibu Ibrahim, ya gargadi masu neman shiga yiwa kasa hidima, da su guji siyasar bangaranci.
Shugaban hukumar, a cewar mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a, Emeka Mgbemena, ya yi wannan gargadin ne a cikin sakon sa ga masu neman shiga yiwa kasa hidima Zango na “Batch C Stream 2” da suka isa sansanonin wayar da kan jama’a a fadin kasar ranar Laraba.
A lokacin da yake jawabi ga wasu mambobin masu yiwa kasa hidima da ke neman ƙaura bisa la’akari da matsalolin lafiya da auratayya, ya ce kowace matsala za a bi ta bisa cancantar ta.