Shugaban rundunar sojin sama CAS), Air Marshal Oladayo Amao, ya nemi rundunarsa musamman matuka jiragen sama da su jajirce wajen yaki da ta’addanci a arewa maso gabashin kasarnan da ma sassan kasar.
Amao ya yi wannan kiran ne a yayin aika sakon Easter day a aikawa rundunar ta shit a Operation Lafiya Dole a Maiduguri. Inda ya nemi da su sadaukar da kuma jajircewa wajen yaki da ‘yan ta’adda.
Ya ce duk da munanan abubuwa da suka faru a ‘yan kwanakin nan na hare-hare, dole ne rundunar ta nuna jajircewa har sai sun tabbatar da sun samar da zaman lafiya a arewa maso gabashin kasar, tare da karar da dukkanin sauran ‘yan ta’adda.
Ya ci gaba da cewa; sun cimma nasarori da dama wajen dakushe karfin ‘yan ta’addan, amma ya ce akwai bukatar a kara sanya azama wajen cimma nasarar samar da zaman lafiya da tsaro a yankin.