Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya sake yin wani kato bara yayin yakin neman zabensa na shugaban kasa a Legas ranar Asabar.
A lokacin da yake jawabi ga dimbin magoya bayansa a mahaifarsa ranar Asabar, tsohon gwamnan Legas ya bukaci magoya bayansa da su je su dauki katin su na “APV”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dan takarar Gwamnan Jihar Sokoto Na Jam’iyyar PRP Da Wasu Jiga-Jigan Jam’iyar Sun Koma APC
Duk da cewa, ana ganin cewa yana nufin Katin zabe na dindindin (PVC) ne, dan takarar shugaban kasa ya daidaita kalaman nasa inda ya kara cewa APC.
“Kina sona? Kana sona? Ku je ku dauki APV…APC ku kada mun kuri’a,”
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya gamu da kura-kurai da dama yayin da yake jawabi ga jama’a a ‘yan kwanakin nan.
A farkon wannan watan ne, yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da yakin neman zabensa a jihar Filato, ya karkare jawabinsa, da cewa, “Allah ya taimaki PD…APC.”
A wani labarin kuma, Lionel Messi Ya Kamo Maradona A Wani Tarihi
Kyaftin din Argentina, Lionel Messi, a ranar Asabar da daddare, ya kamo tarihin da gwarzon dan wasan kwallon kafa, Diego Maradona ya kafa na cin kwallaye takwas a Albiceleste.
Messi ya samu nasarar ne bayan ya zura kwallo a raga a gasar cin kofin duniya da Argentina ta doke Mexico da ci 2-0.