Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai, ya sake yin kira ga sojojin Najeriya da su taimaka wajen kai hare-hare ta sama a maboyar ‘yan ta’adda tare da lalata su domin ceto kasar.
Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a matsayin babban bako a taron makon horas jami’ai soji na kwanaki biyar (CAT) na shekarar 2022 wand rundunar sojojin Najeriya (NA) ta shirya a Jaji, dake jihar Kaduna, a jiya talaat.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan tsaro da kula da harkokin cikin gida Samuel Aruwan, ya bukaci da a ci gaba da gudanar da ayyukan hadin gwiwa na yaki da yan ta’addan.
Ya ce, “Kamar yadda muka sani, Nijeriya a halin yanzu tana fuskantar kalubale masu yawa na tsaro wadanda suka kawo cikas ga ci gaban kasa. Don haka yana da kyau mu hada kai don yakar abokan gaba na hakika, domin dawo da martabarmu da martabar kasa.”
Gwamnan ya yabawa rundunar sojin kasar kan hana yin barna a harin da ‘yan ta’addan suka kai kan jirgin Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris inda fasinjoji tara suka mutu tare da sace 62.
Ya kuma bukaci hukumomin tsaro da kada su yi kasa a gwiwa wajen ganin sun gano wadanda suka aikata wannan danyen aikin domin gurfanar da su a gaban kuliya.
A wajen taron, babban hafsan sojin kasa (COAS), Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya bayyana cewa hadin kai da hadin gwiwa da ba a taba ganin irinsa ba a tsakanin sojojin na kasa da na masu sulke, zai karawa rundunar kwarin gwiwa wajen kaskantar da dukkan abokan gaba.
Ya ce kawo yanzu sojojin sun samu nasarori da dama a wasu hare-hare duk da wasu kalubalen da ake fuskanta.
Ya ba da tabbacin cewa ta hanyar horarwa mai inganci, tsare-tsare mai inganci da samar da ayyukan yi bisa, za a samu nasara a kan masu tada kayar baya cikin kankanin lokaci.
Kwamandan Rundunar Sojojin, Manjo Janar Victor Ezugwu, ya ce taron CAT na bana ya kara jaddada bukatar sake duba dabarun rundunar.