Malam Yohana Jigo, Hakimin Nuku dake yankin Abaji a birnin tarayya Abuja, ya gargadi al’umma da zubar da bola a duk inda suka ga dama. Jigo ya yi wannan kiran ne a yayin ganawarsa da manema labarai a ranar Alhamis a garin Abaji a lokacin da yake sanya ido wajen kwashe bola a yankin.
Ya nuna takaicinsa na yadda bola ya yi yawa a yankin, inda ya dora laifin kan yadda ake zubar da shara a ko’ina.
Ya kara da cewa; duk da kokarin karamar hukumar wajen ganin an rika tsaftace muhalli, amma ana samun wadansu mutane suna gaza bin dokokin share muhallan. Sai dai ya ce karamar hukumar na iya bakin kokarinta wajen ganin an wayar da kan jama’a akan muhimmancin tsafta.