Gwamna Tambuwal na jihar Sakkwato a ranar Lahadi ya shawarci iyaye da su tarbiyyantar da ‘ya’yansu da kuma yaran da suke karkashinsu.
Tambuwal ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da Malam Muhammad Bello, mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai ya fitar, inda ya ce gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin wadanda suka yi nasarar musabakar Alkur’ani mai girma a jihar.
‘Yan Sakkwato shida ne suka yi nasara a bangarori mabambanta a musabakar, inda za su halarci musabakar ta kasa da zai gudana a Kano.
Sunayensu shi ne: Zainab Tambari, Ruqayya Usman, Nura Bello, Hauwa’u Abubakar, Ummulkhairi Abubakar da Abdullahi Muhammad. Tambuwal ya nemi da su zage damtse domin yin nasara a gasar ta gaba.