Ku koyi Sana’a, ku daina ta’addanci da sunan Yajin Aikin ASUU — Wani Shugaba ya gayawa Ɗalibai
Shugaban Ƙaramar Hukumar Oye na Jahar Ekiti Mr. Sunday Ajimoko ya shawarci Ɗalibai dasu guji shiga domin aikata munanan ayyuka, biyo bayan dogon yajin aikin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya.
Ajimoko ya bada shawarar ne a lokacin da yake tattaunawa da ƴan Jarida a Oye-Ekiti na ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bayan shekaru 5, Ƴan Sandan Imo sun kama Bokan daya kashe Sufeton Rundunar
Yace abin damuwa ne yanda yajin aiki ya tsare Dalibai a gida, a yayinda suka kasance basu da sana’a da wani abu da suke yi.
Ya gargadi Ɗalibai musamman ƴan Asalin garin Oye-Ekiti dasu guji ayyukan ta’addanci da suka haɗa da garkuwa da mutane, shan miyagun ƙwayoyi, da sata, da Damfara a yanar gizo, da fyaɗe, wanda ka iya lalata rayuwar su.
Shugaban yace rashin sani ba abu bane da Kotu ke yarda dashi, yana mai ƙara dacewa babban matakin da Ɗalibai da zasu yi a lokacin zaɓen shine domin su samu sana’a da suka haɗa da Ɗinki, da gyaran gashi, da Aski.
“A matsayina na Uba, kuma ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki a ɓangaren Ilmi, ina kira a gareku da ku guji aikata ta’addanci a lokacin wannan yajin aikin na ASUU.
A cewar sa, samun sana’a zai taimakawa Ɗalibai wajen ganin suna cigaba da yin wani abu har sai zuwa lokacin da ASUU ta janye yajin aiki.
Comments 1