Hukumar Kidayar jama’a ta Kasa ta gargadi masu kidaya ta da su guji tsoma kansu ascikin siyasa, da kuma taka-cancan kan lamuran tsaro, duba da irin yadda jihar Borno ta ke a halin yanzu, yayin da ta fara gwajin na’urorin zamani a fadin kananan hukumomi 9 na jihar.
Kwamishinan hukumar dake kula da jihar Borno, Barista Isa Audu Buratai, ne ya yi wannan gargadin lokacin da yake zantawa da manema labarai a yayin bikin kaddamar da fara kidayar gwaji a Maiduguri ranar Talata.
Sai dai Buratai ya bayyana cewa an zabo masu kidayar jama’a 45 a fadin kananan hukumomi 9 na jihar inda za a gudanar da kidayar gwajin.
Ya kuma bayyana kananan hukumin kamar haka: Kukawa, Nganzai, Marte, Mafa, Jere, Ngala, Biu, Hawul da Chibok.
A wani labarin kuma na daban.
Yanzu-Yanzu: Dan majalisar jihar Oyo, Olusegun Popoola ya rasu
Dan majalisar dokokin jihar Oyo, Ademola Olusegun Popoola ya rasu.
DAILY POST ta tattaro cewa Popoola ya mutu ne da sanyin safiyar yau Laraba.
Dan majalisar dai yana wakiltar mazabar Ibadan ta kudu maso gabas II a majalisar dokokin jihar Oyo.
Wakilin majiyar jaridar Dimokiradiyya ya ruwaito cewa dan majalisar ya rasu ne a asibitin Kwalejin Jami’ar (UCH) Ibadan.
An zabi dan majalisar ne a shekarar 2019 domin wakiltar yankin a jam’iyyar PDP.
Rahotanni sun nuna cewa dan majalisar ya rasu ne bayan ya yi fama da cutar koda.
Ya rasu yana da shekaru 46 a duniya.
Kafin rasuwarsa Popoola shi ne Shugaban, Kwamitin Majalisa kan Al’amuran Kananan Hukumomi da Sarautun gargajiya.
Oyekunle Oyetunji, mai baiwa kakakin majalisar dokokin jihar shawara kan harkokin yada labarai, Adebo Ogundoyin, ne ya tabbatar da rasuwar dan majalisar a safiyar yau Laraba.
Ya ce, “Na’am. An tabbatar”.