Rundunar sojin Najeriya ta kawar da fargabar mazauna birnin Maiduguri na jihar Borno, sakamakon wasu bama-bamai da suka tashi a cikin birnin.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ya ce ‘yan ta’addan sun yi yunkurin ci gaba da samun karfin fada-a-ji ne a wajen babban birnin jihar.
Nwachukwu ya bayyana cewa, dakarun rundunar hadin gwiwa ta JTF dake shiyyar Arewa maso Gabas, da na Operation Hadin Kai (OPHK) sun mayar da martani mai inganci kan matsalar tsaron, inda ya bukaci mazauna garin da kada su firgita.
“Wannan mummunan lamari ya haifar da barna da fargaba a wuraren zaman al’uma. Ko da yake, ba a rasa rai ba, abin bakin ciki ne wani dan karamin yaro yaji rauni sanadiyar harin,” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rasha ta Sha Alwashin Tallafawa Nigeria Wajan Magance Matsalar Tsaro
Kakakin rundunar ya bayyana cewa, sojojin kasa tare da hadin gwiwar rundunar sojin sama ta OPHK, sun mayar da martani cikin gaggawa tare da mamaye yankin da kuma yin nasarar kawar da barazana, da yunkurin kutsawa birnin da ‘yan ta’addan su kayi.
“An kuma umarci mutanen Maiduguri da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na zamantakewa da tattalin arziki tare da bayar da bayanai masu inganci kan motsin wadannan miyagun Yan tada kayar baya,” in ji shi.
Comments 1