Ku Magance Matsalolin tsaro, Talauci a Arewa —Wata Ƙungiya ga Manyan Arewa
Wata Ƙungiya da ake kira Arewa Transformational Leaders tayi kira ga Gwamnatoci a Arewa, dasu ƙara azama domin yin gaggawar magance matsalar tsaro, Talauci da Faɗan Addini a yankin.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga ƴan Arewa dasu zauna lafiya, tare da mutunta juna musamman a tsakanin sauran Addinai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’an Soji Sun Kashe Yan Tawayen IPOB 4 A Jihar Imo
Ƙungiyar ta kuma shaidawa ƴan Arewa akan buƙatar dake akwai na yin Kyakkyawan mu’amala da wasu ƴan Ƙasar daga yankin Kudu, da manufar inganta zaman tare da gujewa rabuwar ta.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar baya taro da aka sanarwa Manema labaru daga Sakataren Ƙungiyar Ambasada Dr. Simon Dolly bayan an gudanar da wani taron gaggawa a Abuja.
A cewar Ƙungiyar Arewa tare wasu ɓangarori daya kamata Shuwagabannin Arewa su ƙara baiwa fifiko sun haɗa da, Adalci, Ilmi, samar da masana’antu a yankin.
Comments 2