Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi MURIC tayi kira da’a zamanto cikin haƙuri a Sokoto akan zanga-zangar da akayi akan kisan Deborah Samuel.
Ƙungiyar Musluncin ta gayawa masu zanga-zangar dasu mutunta Sultan Na Sokoto Sa’ad Abubakar, Sarkin Musulmi na Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zamu bada mamaki ga Wanda suke raina mu — NNPP
Daborah, ƴar aji 299 a Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari an kashe ta a ranar Alhamis biyo bayan kalaman data faɗa akan Annabi Muhammad Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi.
A ranar Asabar, masu zanga-zangar suka yi ƙawanya akan tituna domin neman a sako waɗanda aka kama sakamakon kisan nata.
Rundunar Ƴan Sanda ta sanar da cewa ta kama mutane biyu a magarƙamar ta. Har yanzu babu labarin cewa ko an ƙara kama wasu.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Ƙungiyar Farfesa Ishaq Akintola ya fitar, ya bayyana cewar yanzu ba lokaci bane na faɗa da juna, da rarrabuwar kai.
“A matsayin gari na Sarkin Musulmi, dole mu tabbatar Jahar Sokoto ta zamanto cikin kwanciyar hankali.
“Dole a ƙyale Jahar ta cigaba da fuskar kowane Al’amari da suka haɗa da tattalin arziki.
Akintola yace Muslimi a faɗin Najeriya “suna da giramamawa da mutuntawa” ga Sultan.
“Muna buƙatar irin haka daga Matasan Sokoto”, Inji sanarwar.
Comments 1