Gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello a ranar Lahadi ya bukaci jami’an gwamnati su duba yadda suke kashe kudi don su rage.
Sakatariyar yada labaran gwamnan, Mary Berje ce ta fadi haka a cikin wata takardar manema labarai. Ta ce, Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen wani taron kara wa juna sani da aka shirya wa wadanda gwamnati ta raba wa mukamai a kwanakin nan.
Ya bayyana taron a matsayin wanda aka yi a lokacin da ake bukata ga kuma dimbin ilmantarwa, ya kuma yi kira da jami’an gwamnati da su toshe duk wata hanyar da za ta jawo a barnatar da kudin gwamnati.