An shawarci mata masu juna da su rika kwana a cikin gidan sauro domin rage kamuwa da cutar Maleriya da kuma mutuwa da masu juna biyu kan yi.
Alhaji Abdullahi Nageri, Manajan shirin kawar da cutar Maleriya na jihar Kwara, shi ne ya ba su wannan shawarar a yayin da yake zantawa da mannema labarai a garin Omu-Aran dake Kwara.
Nageri ya ce cutar Maleriya tana daya daga cikin cututtuka da suke kashe mata masu juna biyu a fadin kasarnan.
A cewarsa, samun juna biyu na sanya garkuwar kare cututtuka na mata yin sanyi, wanda hakan ke sanya mata masu juna biyu saurin kamuwa da cutar Maleriya. Nageri ya ce a kokarinsu na ganin sun dakile yaduwar cutar Maleriya a tsakanin masu juna biyu, ya sanya suka raba gidan sauro ga mata masu juna biyu guda 100.