Gwamnatin Tarayya ta dorawa Gwamnonin alhakin su tabbatar da samar da isassun magudanan ruwa a Jihohinsu daban-daban domin kaucewa yawaitar ambaliyar ruwa a kasar nan.
Ministar agajin gaggawa, kula da bala’oi da ci gaban al’umma Sadiya Umar Farouq ta yi wannan kiran a ranar Alhamis din nan a wajen kaddamar da rabon kayan agaji ga wadanda bala’in ambaliyar ruwa ya shafa.
Ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya damu kan ambaliyar ruwan da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama da asarar dukiyoyi a kasar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ministar ta bayyana cewa, za a iya magance ko rage yawan afkuwar ambaliyar ruwan sama ta hanyar samar da magudanan ruwa, da tabbatar da ingantaccen amfani da filaye bisa ka’ida.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/alummar-legas-zasu-sami-wutar-lantarki-na-saoi-24/
“Bari in yi amfani da taron na yau don neman goyon bayan kowa don hana sake faruwar ambaliya a nan gaba da kuma tabbatar da cewa ya zo da karamin tasiri”
“Don haka ina kira ga Jihohi da Kananan hukumomi da su ci gaba da samar da magudanan ruwa, da tabbatar da ingantaccen amfani da filaye bisa ka’ida”.
“Ina kuma umartar al’umma da su kula da magudanun ruwan da suke da shi tare da kaucewa ambaliay rafuka da kwanguna,” in ji ta.
Ta ce kayayyakin tallafin da suka hada da kayan abinci da kayan gini don karawa kokarin gwamnatin jihar Jigawa ne na bayar da agajin gaggawa ga wadanda abin ya shafa da kuma saukaka musu wajen yin gyaran cikin gaggawa.
An bayyana cewa mutane bakwai ne suka mutu, da dama sun jikkata, daruruwan iyalai sun rasa matsugunansu, amfanin gonaki sun lalace.
Nigeriantracker