Ku sanya buƙatar kafa Ma’aikatar Dabbobi, wasu buƙatu namu, ko ku rasa ƙuri’un mu – Fulani Ga Ƴan Takara
Wata Kungiyar Fulani Makiyaya Kulen Allah KACRAN ta bukaci ƴan takarar Shuwagabancin Najeriya dasu sanya cigaban Makiyaya daga cikin tsare-tsare da shirye-shiryen ko kuma su rasa ƙuri’un su a Babban zaɓe mai zuwa.
Shugaban Ƙungiyar KACRAN Khalil Mohd Bello ya bada wannan umarnin a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata a Damaturu.
Ƙungiyar ta lura tare da damuwa yadda duk da irin gudunmawar da suke bayar wa wajen cigaban tattalin arzikin Najeriya da kuma samar da abinci mai gina jiki, amma an ƙyale su idan aka zo ga batun tsare-tsare da shirye-shirye.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilin Da Na Ƙi Fita Jinya Ketare —Osinbajo
“Da yawa daga cikin ƴan kasuwa, idan ka cire ƴan Jahohi kaɗan, basu damu da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen Cigaban bangaren dabbobi na samar da miliyoyin ayyukan yi ga Matasa da Al’umma wanda suka dogara da sana’ar.
“KACRAN, ta lura cewa sai an ƙirƙiri Ma’aikatar Albarkatun Dabbobi sannan za’a magance wasu matsaloli da suka jibanci ruwa da Abincin Dabbobi a lokacin rani.
“Ma’aikatar Noma da Cigaban Yankunan Karkara ita keda alhakin buƙatun su, wanda ya hana su kawo cigaba ta ɓangaren Dabbobi, a saboda haka akwai buƙatar kafa Ma’aikatar Kula da Cigaban Dabbobi.
Shugaban Ƙungiyar ya taya Asiwaju Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Rabi’u Musa Kwankwaso, da Peter Obi, da suka samu nasarar zama ƴan takarar shugabancin Najeriya sai yayi kira a garesu dasu sanya bukatun cigaban Dabbobi a cikin tsare-tsare da shirye-shiryen su.