Babbar Ƙungiyar Ƴan Ƙabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo Worldwide, ta ce ya kamata Majalisar Dokokin ƙasar ta tsige mataimakin Shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo tare da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Ohanaeze ya ce Buhari da Osinbajo sun gaza a babban nauyin da ya rataya a wuyansu na kare ƴan Najeriya.
Ƙungiyar ta ce gazawar Buhari da Osinbajo na kare ƴan Najeriya ya nuna gazawar Shugabanci a Harkokin Mulki.
Idan dai za’a tuna cewa Sanatoci sun yi barazanar mika wa Buhari sanarwar tsige shi kan gazawarsa wajen Magance Matsalar rashin tsaro a ƙasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Peter Obi ya bayyana abin da zai yi idan Yaƙi ya Ɓarke a Najeriya
Ɓangaren Marasa Rinjaye na Majalisar Dattijai sun bai wa Buhari wa’adin makonni shida ya Magance Matsalar Rashin Tsaro a Ƙasar.
Da yake mayar da martani, Ohanaeze ya ce, Bola Tinubu, jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Ɗan Takarar Shugaban kasa, zai amfana da wani abu idan har ba’a cire Osinbajo ba.
A wata sanarwa da Babban Sakataren ta, Okechukwu Isiguzoro, Ohanaeze ya fitar, ya gargaɗi Majalisar Dokokin ƙasar cewa “idan har barazanar tsige shugaba Buhari ya kamata a dauki matakin tsige wa da muhimmanci, don Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osibanjo ya kasance cikin shirin tsige shi, domin dukkansu sun gaza wa Ƴan Najeriya.
“Keɓance mataimakin shugaban ƙasa, daga barazanar tsige shi, ya nuna cewa Ɗan Takarar Shugaban ƙasa na APC, Bola Ahmed Tinubu ya kasance babban wanda zai amfana.”
Ohanaeze ta ce Osinbajo na iya haifar da kura-kurai da za su baiwa Tinubu goyon baya a zaɓen 2023 idan ya zama Shugaban Ƙasa.
“Ndigbo yana tunatar da majalisar kasa cewa yunkurin fara tsige shugaba Buhari ba tare da mataimakin shugaban kasa Osibanjo ba, tsari ne da bai kammala ba kuma zai haifar da wata dama ga Mataimakin Shugaban Ƙasar ya nuna kabilanci idan har shine Shugaba.