A wani mataki na ganin an kawo kashen matsalar fyade da yake ciwa al’umma tuwo a kwarya, an gudanar da taro domin lalubo hanyoyin da za a fadakar da al’umma illar aikata wannan dabi’a ta yin fyade. Taron wanda ya gudanar karkashin Hajiya Asma’u Ahmad Joda a cibiyar inganta rayuwar Mata dake Yola.
Asma’u Ahmad Joda ta ce ya zama wajibi a dauki kwararan matakai domin ganin an kauda wannan dabi’a na yin fyade a tsakanin al’umma wanda hakan ke bata rayuwar al’umma musaman ma wadanda lamarin ya shafa.
A don ta yi kira ga iyaye da su tashi tsaye wajen sa ido akan harkokin ‘ya’yansu wanda a cewar ta su suke da kaso mafi tsoka na magance matsala fyaden baki daya. Asma’u har wala yau ta shawarci jama’a da su taimaka wajen bada bayanai ko kai rahoton aikata lafin fyade ga jami’an tsaron ko wasu kungiyoyi dake baki da yin fyade.
Adamu dodo tare da Umar Hassan Sherpella sun gudanar da jawabai a wurin taron kasancewar su ‘yan jaridu sun kira yi masu ruwa da tsaki da su mara wa ‘yan jaridun baya da hadin kai domin ganin ‘yan jaridun sun samu kwarin gwiwa wajen bin diddigin labarin aikata fyaden.