Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma ya gargadi sabbin kwamishinoninsa da ya rantsar a jiya talata cewa su shafa wa kansu, don gudun faruwar abinda ya faru da yan bayansu.
Uzodinma yana wannan magana ne a yayin rantsar da Kwamishinonin da saura shugabannin sasssan Gwamnati daban-daban da ya rantsar.
Ya ce shi ba zai zura idanu kawai ya ga ana wa-kaci-wa-tashi da dukiyar al’umma ba, don haka duk wanda ya kama da kashi a duwawu to lallai zai dandana kudarsa.
Vikin wadanda aka rantsar din akwai tsohon mataimakin gwamnan jihar Ada Okwuono wanda aka bashi shugaban hukumar ilmin bai daya ta Jihar wato IMSUBEB.
Gwamnan ya kara da cewa a yanzu hala ya shirua tsaf don aiwatar wa al’ummar jihar ayyuka da zai zamo musu romon Dimokuraɗiyya