Gwamnan jihar Kaduna kuma Shugaban yakin neman zaben jam’iyyar APC a jihar Kogi, Nasiru El-Rufai ya roki mutanen jihar Kogi da su sake zaben Gwamna Yahaya Bello a karo na biyu.
El-Rufai ya roki mutanen jihar Kogi da su yafe wa Gwamnan a kan wasu abubuwa da ya yi musu kuma suke kallo a matsayin kuskure sannan su bashi damar zarcewa a zaben ranar Asabar karkashin inuwar APC.
Ya yi rokon ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron gama-garin da jam’iyyar ta shirya a filin kwallon kafa na Confluence a garin Lokoja a ci gaba da yakin neman sake zaben gwamnan a karo na biyu.
A cewar El-Rufai, ba a iya raba matasa da kuskure. “Idan mutum matashi ne, yana kura-kurai. Ina rokonku, gani a gwiwowina. Ku yi hakuri ku yafe mishi dukkan kura-kuran da ya yi muku.
Ina rokonku. Mu ajiye tarihi. Kar mu bata tarihin marigayi Prince Abubakar Audu ta hanyar barin jam’iyyar PDP ta karbi jihar na. Dole mu yi aiki don hadin kai da ci gaban jihar Kogi,” inji El-Rufai.
El-Rufai ya ce yawon yakin neman zaben nan da suke ba wai kawai neman dawowar Yahaya Bello suke ba, a lokaci gudu kuma jana’izar jam’iyyar PDP suka fito yi, wanda a cewarshi a tsawon lokacin da suka mulki jihar babu wani aikin da suka yi.
Ya ce ayyukan da Yahaya Bello ya yi a shekaru 3 ya fi abin da PDP ta yi shekaru 13.
Daga karshe ya bukaci mutanen jihar da su zabe Sanata Smart Adeyemi, kada su maimaita kuskuren da suka yi a baya.