Gwamnatin jihar Kano ta ayyana neman mawakin da ake kira da 442 ruwa a jallo, saboda yin wakokin da basu dace ba.
Shugaban hukumar tace fina finai ta jihar Kano, Isma’il Afakallah, ya bayyana cewa wakokin sun sabawa da dokar hukumar.
Ya roki al’umma da su taimaka wajen kama mawakin da kuma Tsohuwar jarumar Kannywood Safara’u domin gurfanar dasu a gaban kotu.
Afakallah ya kuma bada umarnin dakatar da kunna wakokinsu a wuraren biki da taruka baki daya.
KARANTA ANAN: CAN, Babban Limami Sunyi Allah-Wadai da kisan Sheik Goni Aisami
Mawakan wadanda suka hada da Safara’u da Mista 442 na samun tarin mabiya a yan watannin nan mussaman a shafin Tik-tok.
Safara’u wacce asalin sunanta shi ne Safiya Yusuf, ta fara shahara ne a cikin shirin Kwana casa’in na gidan talabijin na Arewa24.
Ta fita daga shirin ne bayan bullar wani Bidiyon tsiraici da ake zarginta da shi.
Shima 442 wanda asalinsa dan Zaria ne a jihar Kaduna, sunansa na asali ne shi ne Mubarak Abdulkarim.
A wani labarin kuma: “Ya kamata A Wargaza Kungiyar ASUU, Ba Ta Da Amfani”—–Dan Gwamnan Jihar Kaduna
Bashir, daya daga cikin ‘ya’yan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar Litinin, ya bayyana kungiyar malaman jami’o’i ta kasa wato ASUU a matsayin “kungiyar da ba ta da amfani”, inda ya cigaba da cewa ya kamata a wargazata a maye gurbinsu da malamai masu kula da damuwar dalibai.
Hakan na zuwa ne bayan ASUU ta yanke shawarar tsawaita yajin aikin da take yi.