Ku Taimakamana Wajan Magance Matsalar Tsaro— Shugaba Buhari Ga Kasashen Duniya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yaba wa kokarin da kasashe ke yi wajen tunkarar kalubalen tsaro a fadin duniya, ciki har da Najeriya, inda ya bukaci karin hadin gwiwa don dakile ayyukan ta’addanci, ‘yan fashin daji da kuma yan tada kayar baya.
Buhari ya bayyana haka ne a Abuja, yayin da yake karbar wasikar amincewa da Jakadan kasar Canada a Najeriya Ambasada James Kingston Christoff da jakadan kasar Mexico a Najeriya, Juan Alfred Miranda Oritz.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa shugaba Buhari ya shaidawa jami’an diflomasiyyar cewa an samu nasarar dakile matsalar rashin tsaro ta hanyar hadin gwiwa a kan iyakokin kasar, kuma za a iya cimma hakan a sauran sassan kasar nan.
“Mummunan tasirin rashin tsaro a duniya, sauyin yanayi da kuma Cutar COVID-19 da ta lalata tattalin arzikin duniya baki daya.
Ya kara da cewa, Kasashe na ci gaba da kokawa don murmurewa daga wadannan kalubale wanda da dama daga cikinsu lamarin ya shafesu a duniya.
“Yakin da ake ci gaba da yi tsakanin Rasha da Ukraine ya kawo cikas ga ci gaban da kasashen suka samu wajen magance matsalar abinci a cikin shekaru goma da suka gabata. ” inji shi
A cewar Buhari wutar rikicin siyasa a kasar Libya na ci gaba da ruruwa, inda ta’addanci a yankin Sahel, tare da dakile hanyoyin samar da ababen more rayuwa na dimokuradiyya a yankunan yammacin Afirka da tsakiyar Afirka yayi kamari.
A matakin yankin, Shugaba Buhari ya ce Najeriya ta yi aiki tare da sauran kasashe mambobin ECOWAS da sauran kungiyoyin nahiuar Afrika, domin magance matsalolin hare-haren ta’addanci, hare-haren kan iyakan tudu dana Ruwa, da suka hada da fashin teku da kamun kifi ba bisa ka’ida ba a cikin rafi.
Shugaban ya bukaci jami’an diflomasiyya da su sanya ido kan harkokin siyasar a kasar nan a yayin zaben Shwkarar 2023, amma su ci gaba da bin ka’idojin aikinsu na rashin tsoma baki kan harkokin cikin gida.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa Najeriya na kara kusantowa da zabukan kasarta, kuma ‘yan takara masu wakiltar jam’iyyunsu a matakai daban-daban sun fara samar da daidaito a tsakanin jam’iyyunsu a shirye-shiryen kaddamar da yakin neman zabe a fadin kasar nan ba da dadewa ba.
Shugaban ya kuma shawarci jami’an diflomasiyyar da su mai da hankali wajen inganta nasarorin da magabatansu suka samu.
A nasa jawabin, a madadin jakadun, Jakadan kasar Canada ya godewa shugaban kasar bisa bikin karbar wasikun nasu.