Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, CNOL, yayi Kira ga mawadata su tallafawa kokarin gina Jami’o’i masu Zaman kansu da wasu mawadata keyi a jihar Kano.
Alhaji Aminu Ado Bayero yayi wannan Kiran ne a wajan taron Kaddamar da littafin tarihin rayuwar Shugaban rukunin kamfanonin AZMAN Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina wanda aka yiwa lakabi da (RESILIENCE) aka kuma gudanar da taron a dakin taro na Jami’ar Bayero dake Kano.
KU KARANTA: Matasan Arewa Sun Bukaci Buhari Ya Gaggauta Tsige Shugaban DSS
Mai martaba Sarkin yace gina irin wadannan jami’oi a masu Zaman kansu a jihar Kano zai taimakawa dalibai su samu guraben karatu bayan kammala makarantun sakandire.
A don haka ne ya yabawa Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina bisa samar da wannan jami’a, Yana mai cewa hakan zai cigaba da habaka ilimi a jihar Kano, tare da godewa wadanda suke akan gaba wajan gina irin wadannan jami’oi masu Zaman kansu.
Alhaji Aminu Ado Bayero yace a shekarun baya an samar da kamfanonin jiragen Sama wadanda suka hadar Kabo da Freedom da IRS air, inda yace yanzu kuma akwai Azman da Rano air, kuma dukkaninsu kamfanonin jirage ne na “yan asalin jihar Kano.
Yayi bayanin cewa suna bayar da gudummawa kwarai da gaske, amma yaja hankalin kamfanonin jiragen da suka rage suyi duba na tsanaki domin dubawa da gyara irin kura kuran da aka samu a baya domin samun nasara.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero daga bisani yayi Kira ga al’uma su cigaba da jajircewa wajan yiwa Najeriya addu’oin samun Zaman lafiya da hadin kan al’ummar wannan kasa, ya kuma yi addu’ar zabuka masu zuwa Allah yasa ayi su lafiya a gama lafiya tare da zaba mana shugabanni nagari.
A wani labarin kuma: Hukumar Hisbah Tayi Nasarar Tarwatsa Wani Auren Jinsi Da Aka Shirya Ɗaurawa A Kano
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta yi nasarar dakile auren da aka shirya daurawa a tsakanin, Mujahid da Abba wadan da ake zargi da “Yan daudu ne.
Wata majiya ce mai karfi ta sanar da hukumar Hisbah, Bikin Auren Wanda a ka shirya Yi a Daren ranar Litinin, a Wani gidan Event Center da ke bayan, Dogon Banki a Birnin Kano.
Dakarun Hukumar Hisbah sun Sami nasarar kama “Yan mata 15 da samari 4 ciki har da Mai gidan Event Center din, da wata budurwa Mai suna Salma wacce ake zargi da kitsa bikin domin ya yi kama da bikin birthday.