Daraktan yada labarai na hukumar tsaro ta kasa, Manjo Janar Jimmy Akpor, ya yi kira ga kafafen yada labarai da su taimaka wajen Bai wa sojojin da aka tura zuwa ayyuka daban-daban a fadin kasar nan da bayanai.
Akpor ya ce hakan zai baiwa sojojin damar kare martabar yankunan kasar yadda ya kamata tare da samun nasara a yakin da ake yi da ‘yan tada kayar baya a Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa hakan zai kasance mafi kankantar gudumawar da ‘yan jarida za su bayar wajan yakara matsalar tsaron kasa.
Akpor ya bayyana haka ne bayan da ya fara aiki ranar Juma’a a hedikwatar tsaro da ke Abuja.
Ya ci gaba da cewa, “idan aka yi la’akari da cewa tsaron kasa ya kunshi Kare Yan kasa, Bunkasa tattalin arzikinta, da sauran cibiyoyi, yayin da sojoji da sauran hukumomin tsaro sun kasance a sahun gaba wajen tabbatar da ‘yancin da kasar ke da shi, iyakokin kasa. da kuma samar da hanyoyin samar da tsaro a fannin tattalin arziki, siyasa da makamashi, da dai sauran abubuwan da suka shafi tsaron kasa.
“Ya kamata Mu San abubuwan da ke tattare da mahimmancin faɗakarwa, wajen inganta bangaren ɗabi’a, wanda ke ba ma’aikata damar yin yaƙi yadda ya kamata, da jajircewa da wajan tunkarar duk wata matsala, yayin da suke gudanar da ayyukansu na tsarin mulki. Don haka ‘yan jaridunmu, su yi nasu bangaren (kamar yadda kuka saba yi), wajen dorewar tarbiyyar ‘yan kasa musamman ma na soja, tare da sauran jami’an tsaro, a yayin da suke tunkarar kalubalen tsaro na wannan zamani da suke fuskanta.
” Karawa Sojoji kwarin gwiwar da ke fada, da ta’adda, zai kasance muhimmiyar gudunmawar ku ga sha’anin tsaron kasa a matsayinku na ‘yan jarida.” Inji shi