Daga: Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci al’umma da malaman addini da su yi Allah-wadai da kuma tashi tsaye wajen yakar kashe-kashen da ake yi a yankin Kudu maso Gabas kamar yadda Jaridar Daily Post ta rawaito.
Buhari ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Asabar a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikicin PDP: Atiku Da Wike Sun Amince Da Kwamitin Mutane 14 Don Shiga Tsakani
Shugaban ya bada tabbacin cewa ana gudanar da dukkan matakai da bincike domin gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kuliya.
Jawabin na Buhari ya zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa an kashe wasu ‘yan kasar Nijar guda shida da ‘yan sanda a bakin aiki.
“Ya kamata al’umma da malaman addini su kara yin magana da karfi kan kashe-kashen, mu tashi tsaye mu kare ka’idojin al’adunmu da addini.
“Wadanda suka sani yakamata su nuna takamaiman mutanen da suka yi wannan,” in ji shi.
Ya bayyana jajircewar gwamnatin sa na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin kudu maso gabas da ma kasa baki daya, yana mai cewa rahotannin kashe-kashe a ko’ina abin bakin ciki ne da rashin jin dadi.
Shugaban ya jajantawa iyalan jami’an tsaro da aka kashe da kuma gwamnati da al’ummar Jamhuriyar Nijar wadanda aka sare kawunansu.