Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NIHSA) ta yi kira ga jihohin kasar da su yi shirin tarben ambaliyar ruwa mai yawa a sakamakon ruwan sama da za a yi ta dibgawa kamar da bakin kwarya a dan wannan tsakanin nan gaba kadan. Babban daraktan hukumar, Injiniya Clement Nze, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Laraba. Ya ce, a na sa ran samun ambaliyar ruwa sosai a sakamakon ruwan sama mai yawa da a ke tsammatan faruwarsa a sassan kasar a yanzun haka. Nze ya ce, rafika za su fara tumbatsa su na ambaliya ne a watan gobe a sabili da karuwar ruwan saman da za a samu daga Kogin Neja da na Binuwe. Ya ce, akwai alamu sosai a wannan karon za a sami karin jihohin da za su fuskanci ambaliyar ruwan a watanni masu zuwa.