Tsohon shugaban Kasar Najeriya, Abdul-Salam Abubakar, ya roki Yan bindiga da su ajiye makaman su, su zo su rungumi zaman lafiya. Kamar yadda Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
Abdul-Salam Abubakar, ya bayyana hakane jim kadan bayan kammala babbar Sallah lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna.
“Ina addu’a Allah ya karkato kan wadannan Yan bindigan su ajiye makaman su, su bar satar mutane, fashi da makami, kore shanun mutane da sauran nau’ikan ta’addanci a kasar nan.”
KARANTA:- Ku taimaka ku sa baki a saki Nnamdi Kanu, Kalaman Ƙungiyar Ohanaeze ga gwamnonin Kudu
Yace matukar za’a sami zaman lafiya to tabbas za’a sami cigaba a kasar nan.
Abdul-Salam Abubakar ya yima daukakin al’ummar Musulmai murnar babbar Sallah.
Ya kuma yi kira ga sauran Yan Najeriya da su zama ma su bin doka gami da son zaman lafiya a kasar.
Haka shima gwamnan Jahar Neja, Abubakar Sani Bello Lolo, yayi kira ga sauran Al’umma da su dage da addu’oi wajan kawo karshen ta’addanci a kasar nan.
Ya bukaci Yan Najeriya da su cigaba da baiwa jami’an tsaro sahihin labari don cigaba da bincike, haka zai taimaka akan tsaron lafiyar mutane a kasar nan.
Haka shima Tsohon gwamnan Jahar ta Neja, Dakta Babangida Aliyu, yayi kira ga gwamnatin kasar nan da su cigaba da tallafawa jami’an tsaro don kawo karshen ta’addanci a kasar.
Ya shawarci shuwagabannin ta kowane fanni a kasar nan, da su fito da hanyoyi daban-daban kan kawo karshen ta’addanci a kasar nan.
Haka shima babban Malami Ibrahim Fari, shine ya jagoranci Sallar Idi a Minna, yayima mutane nasiha da su so zaman lafiya a a duk inda suka sami kansu.
Bayan kammala nasihohi, Malam Ibrahim Fari, nan take ya yanka abun layyar sa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Comments 1