Gwamnna babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele, ya roƙi ƴan Najeriya da su bari tsarin sauya fasalin kuɗi yayi aiki.
Emefiele ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da ƴan jaridar fadar gwamnatin tarayya bayan ya kammala ganawa da shugaba Buhari, a birnin tarayya Abuja. Rahoton jaridar Daily Trust
KU KARANTA KUMA: Ba beli: Kotu tace a cigaba da tsare Murja Kunya a gidan gyaran hali
Yace wahalhalun da ƴan Najeriya ke sha a dalilin tsarin, na wani ɗan lokaci ne, inda yayi nuni da cewa tsarin zai bunƙasa faɗan da gwamnati take yi da cin hanci da rashawa da kuma haɓɓaka tattalin arziƙi.
A kalamansa:
“Maganar gaskiya itace dukkan mu bayi ne. Ƴan Najeriya muke yiwa bauta. Abinda muka sani kawai shine Antoni Janar yayi magana kan lamarin, sannan a yau da safe shugaban ƙasa ya ƙarasa komai akan lamarin.”
“Ina tunanin kawai zan roƙi ƴan Najeriya, mu yi haƙuri mu bar wannan tsarin yayi aiki.”
“Wannan tsarin sabon tsari ne wanda ya rage matsalar cin hanci da rashawa, wannan tsarin ya warware wasu matsalolin tattalin arziƙi, wannan tsarin ya kuma rage matsalar tsaron da ake fama da ita a ƙasar nan.”
“Waɗannan abubuwan uku waɗanda sune manufofin gwamnatin nan suna ƙunshe a cikin wannan sabon tsarin. Kamata yayi kawai mu bari yayi tasiri. Na sha faɗin cewa wannan wahalar ta ɗan lokaci ce, amma ina tabbatarwa da ƴan Najeriya cewa amfanin da Najeriya zata samu daga tsarin yana da yawa.”
Ku Yi Siyasa Ba Tare Da Cin Mutuncin Kowa Ba, Tinubu Ya Gargaɗi Magoya Bayan Sa
A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, ya nemi magoya bayan sa da suyi siyasa bada gaba ba.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Alhaji Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya ja hankalin magoya bayansa kan cewa su yi siyasa mai tsafta ba tare da ɓatanci ko cin zarafin kowa ko ɓatanci ga abokan adawa ba.