Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Alhaji Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya ja hankalin magoya bayansa kan cewa su yi siyasa mai tsafta ba tare da ɓatanci ko cin zarafin kowa ko ɓatanci ga abokan adawa ba.
KU KARANTA KUMA: Samari albarkatu na kawai suke hari, cewar budurwa mai diri da ta kasa samun saurayi na gaskiya
“Mu na da ayyuka birjik da dama waɗanda mu ka yi tsawon shekarun baya, mun gina mutane mun gina ƙasa, mun ba da gudunmawa wajen kyautata rayuwar al’umma ta ɓangarori daban-daban.
Sannan kuma mu na da manufofin da mu ka fitar waɗanda za mu yi amfani da su wajen gina sabuwar Nageriya Saboda haka mu na da abubuwan da sun kai a tallata mu da su cikin mutunci da girmamawa”. Inji shi.
Asiwaju ya kuma ƙara da cewa duk ɗan siyasar da ya yi abin azo a gani, ba ya buƙatar sai an ci mutuncin wani a kansa kafin a tallata shi, domin tarihi shi ke bayyana matsayin mutum da kuma abin da ya yi.
“Idan ka yi wani abu na alkhairi, ko ka na da manufa mai kyau ta yin abin alkhairi to waɗannan sun isa su sayar da kai ga jama’a su zaɓe ka, ba sai ka ci mutuncin kowa ba”. A cewar Tinubu.
Haka kuma, ɗan takarar na shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, ya ƙara da cewa:
“Kowane mutum ya na nuna tarbiya ne irin ta gidansu, mu a gidan siyasarmu babu cin mutunci, babu yarfai, babu ƙage, babu zage-zage da ashar.”
“Mu na siyasa ne bisa dattako, girmamawa da ganin darajar al’umma, saboda haka, ina mai jan hankali da horo ga mabiyanmu cewa a yi siyasa batare da an ci mutuncin kowa ba.”
An yabawa Shugaba Buhari kan umarnin sa na amfani N200
Kungiyar Kungiyoyin farar hula na jihohin Arewa sun bayyana tsawaita wa’adin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na amfani da tsohuwar Naira 200 zuwa 10 ga Afrilu a matsayin shaida cewa yana nufin alheri ga ‘yan Najeriya.
Tsawaita amfani da tsofaffin takardun kudi na Naira 200, kamar yadda suka yi nuni da cewa, zai magance wahalhalun da talakawa ke fuskanta.