Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bukaci jam’iyyar PDP da ta tattauna da , dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP Peter Obi gabanin zaben 2023. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Fayose ya kuma bukaci shugabannin PDP da su sasanta rikicin da ke tsakanin Gwamna Nyesom Wike na Rivers da jam’iyyar .
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalisar Malamai Ta Zamfara Ta Yi Alkawarin Marawa Takarar Tinubu
Tsohon gwamnan ya yi wannan kiran ne yayin da yake jaddada cewa watakila PDP ba za ta lashe a yankin Kudu maso Gabas ba a lokacin zaben shugaban kasa.
Ya yi nuni da cewa Kudu-maso-Kudu za ta kasance hade wuri guda kan muradunta.
Da yake jaddada cewa PDP ba ta da ayyuka da yawa a yankin Arewa ta Tsakiya, Fayose ya ce: “PDP da APC ba su zabi wani dan takara ba, ko dai shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa daga yankin arewa ta tsakiya. Arewa maso gabas ne dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC ya fito.”
Jigon na PDP ya kuma bayyana, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Rabi’u Kwankwaso a matsayin mai wata gibi.
“Za mu baiwa jam’iyyar kuri’un jihar Adamawa. Kar a manta akwai wani mai suna Kwankwaso da ya ke tamkar wata cuta, wanda zai iya samun wasu kuri’u a arewa.
“Yin sulhu ko tattaunawa da Obi zai zama abu mai kyau kuma samun hanyar yin sulhu da Wike zai zama abu mai Mahimmancin gaske” Fayose ya shaida wa Channels Television.
A WANI LABARI KUMA: Moghalu Yayi wani hasashe mai ƙarfi game da Jihohin da kowane Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa zai Lashe
Wani tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar African Democratic Congress, Kingsley Moghalu, ya yi hasashen jihohin da ƴan Takarar Shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Bola Tinubu; dana Jam’iyyar Labour, LP, Peter Obi; da kuma Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, zasu yi nasara sosai.
Moghalu ya yi hasashen cewa Tinubu ne zai samu ƙuri’u mafi rinjaye a jihar Legas, Obi zai samu nasara a jihar Ribas, kuma Kwankwaso ne zai samu mafi yawan kuri’u a jihar Kano