Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki likitocin kasar dake yajin aiki da su yiwa Allah su koma bakin aikin su domin ci gaba da tattaunawa da jami’an gwamnati domin shawo kan matsalolin da suka addabe su.
Yayin ganawa da shugabannin kungiyar likitoci na kasa, shugaban ya kuma roki sauran ma’aikatan lafiya dake shirin tsunduma cikin yakin aikin da su sake tunani akai, inda ya bayyana cewar kasar na matukar bukatar aikin su a wannan lokaci fiye da lokacin da ya shude.
Buhari yace dogon lokacin da ake dauka ana tattauna ya zarce fadawa cikin yajin aiki saboda illar da hakan ke yiwa jama’ar kasa.
Shugaban kasar yace rayukan mutanen dake salwanta lokacin yajin aikin likitocin na da matukar tasiri, saboda haka rungumar hanyar tattaunawa tafi shiga yajin aikin.
Buhari yace a shirye yake ya biya daukacin basussukan da ake bin likitocin da zaran an kammala tantance su, inda ya kara da cewar yajin aikin na su a wannan lokaci ba abinda ya dace ba ne.
Shugaban kasar yace kare lafiyar jama’ar Najeriya ba wai ya rataya bane akan gwamnati kawai, amma hakki ne da ya rataya akan kowanne ‘dan kasa, musamman jami’an kula da lafiya.
Buhari yace tsunduma cikin yajin aikin a irin wannan lokaci ba abu ne mai kyau ba, koda kuwa wane irin matsala likitocin ke fuskanta, ganin yadda ake matukar bukatar aikin su.
Shugaban kasar yace gwamnatin sa na da tarihin biyan basussukan da ma’aikata ke bin ta, ciki harda na ‘yan fansho da ‘yan kwangila, tare da basussukan da suka gada daga gwamnatocin da suka gabata muddin aka tabbatar da sahihancin su.