Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, a jiya, ya bukaci malaman addini su ci gaba da neman taimakon Allah a kan matsalolin Najeriya da ma duniya baki daya.
Gwamna Sanwo-Olu ya yi wannan roko ne a lokacin da ya karbi jagorancin kungiyar Baptist Convention karkashin jagorancin shugabanta kuma babban jami’in gudanarwa Rev (Dr) Israel Akanji.
Gwamnan ya koka da cewa sannu a hankali duniya tana jin sakamakon yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, da kuma tasirin cutar ta COVID-19.
Don haka ya yi kira da a ci gaba da hakuri da addu’ar samun zaman lafiya, hadin kai da tsaro a jihar legas da Najeriya da ma duniya baki daya.
Yayin da yake taya shuwagabannin Baptist murnar babban taron da suke gudanarwa karo na 109, ya mika sakon fatan alheri ga mambobi sama da 20,000 da aka ce za su halarci taron.
Tun da farko, Rev Akanji ya yabawa Gwamna Sanwo-Olu bisa nasarar dakile cutar ta COVID-19 da kuma matakan da aka dauka na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar.
Ya kuma roki gwamnan da ya kammala shirin mayar da makarantar sakandaren Baptist ta Legas, Orile Agege zuwa cocin, sannan ya nemi goyon bayan gwamnatin jihar a wasu ayyuka da cocin ke ci gaba da yi.
A wani labarin Kuma ba daban.
An gurfanar da wasu Mutum biyu a gaban Kotu, kan zargin satar na’urar sanyaya daki
An gurfanar da wasu mutane biyu Joseph Simon mai shekaru 25 da Oseni Meco mai shekaru 22 a ranar Talatar da ta gabata a gaban wata kotun Majistare da ke Ejigbo na jihar Legas.
Wadanda ake tuhumar, wadanda ba a bayyana adireshinsu ba, suna fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hada baki, sata da karbar kayayyakin sata.
Dan sanda mai shigar da kara, Insfecta Benedict Aigbokhan, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar da sauran su, sun aikata laifin ne a ranar 4 ga watan Afrilu da misalin karfe 3:30 na rana, a makarantar koyar da addinin islama ta Soundhope dake Baruwa na yankin Ipaja a jihar Legas.
Ya ce wanda ake kara na farko, Simon, ya saci na’urar sanyaya daki guda hudu, wanda kudinsa ya kai Naira 300,000, mallakar Soundhope International Muslim Academy.
Aigbokhan ya kuma ce wanda ake kara na biyu, Meco, ya karbi kadarorin, da sanin cewa an sace su ne.
A cewar sa, laifukan sun ci karo da sashe na 280(2) da 328 da 411 na dokar laifuka ta jihar Legas ta shekarar 2015.
Wadanda ake tuhumar dai, sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su.
Alkalin kotun, Mrs K.A. Ariyo, ya bayar da belin wadanda ake kara a kan kudi Naira 200,000 kowanne, tare da tsayayyu biyu kowannen su. Kuma ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 10 ga watan Mayun shekarar 2022.