Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bukaci kafafen yada labarai da su yi watsi da masu wa’azin rashin hadin kai, su kuma baiwa masu kokarin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai muhimmanci.
IBB ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya a wani katafaren gidansa da ke Minna.
Ya ce dole ne ‘yan Najeriya su dage wajen yin imani da hadin kan Najeriya tare da rokon su da su yi hakuri da kuma yi wa kasa addu’a domin ya shawo kan kalubalen da ke addabar kasar nan.
Yayin da yake nuna jin dadinsa kan rawar da kafafen yada labaran Najeriya ke takawa, ya yi kira da a sauya fasalin yada wasu labaran domin samun ingantacciyar Najeriya ta hanyar yin abin da ya dace.
Kwanan Nan Za’a Samu Ambaliyar Ruwa A Jihohin Arewa 3 Da Bayelsa, NiMet
Dattijon ya kuma yabawa masu aikin yada labarai a kasar nan kan yadda suke gudanar da ayyukansu na ban mamaki a cikin rahotonsu, nazarin batutuwa da goyon bayan dimokuradiyya mai dorewa wanda dole ne a inganta ta hanyar tafiyar da al’umma.
Tsohon shugaban na mulkin sojan ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu so, jajircewa, rikon amana da addu’a domin kawo karshen kalubalen rashin tsaro da al’ummar kasar ke fuskanta a halin yanzu, inda ya kara da cewa wadanda ke bayan wadannan matsaloli za su gane illar dake tattare da tasirin ayyukansu.