Shugaban Cocin Prelate of the Eternal Sacred Order of Cherubim and Seraphim, David Bob-Manuel, ya bukaci gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i da su kawo karshen yajin aikin cikin gaggawa.
Punch ta ruwaito cewa, Bob-Manuel ya yi wannan kiran ne a ranar Larabar da ta gabata a wani taron manema labarai a yankin Surulere da ke jihar Legas.
KARANTA WANNAN LABARIN: Uba Sani Ya Jagoranci Tantace Mutanen Da Buhari Ya Turo Domin Basu muƙami a CBN
Shugaban ya bayyana a cikin jawabinsa cewa yajin aikin na kawo cikas ga ci gaban bil’adama tare da sanya takardun shaidar da aka samu daga manyan makarantu ba su da wani amfani ko kadan.
Ya ce, “Baya ga rashin tsaro, yajin aikin da ASUU ke ci gaba da yi na daya daga cikin batutuwan da suka fi addabar mutane a Najeriya. ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun a watan Fabrairu, sama da watanni shida da suka gabata. Irin wannan jan kafa a karatun jami’a yana kawo cikas ga ci gaban ɗan adam da kuma sanya takaddun shaida da aka samu daga manyan makarantun ba su da ƙima ko kaɗan.
“Jami’o’in gwamnati, wadanda suka kasance abin farin ciki ga dukkan iyaye, an kai su ga mafi karancin albashi. Ci gaban ilimi mai inganci shi ne ginshikin ci gaban fasaha ga kowace kasa. Bai kamata wata kasa ba ta bar matasanta su daina zuwa makaranta na tsawon lokaci suna yawo a kan tituna suna fuskantar wasu a bubuwa.
“A nan ina kira ga Gwamnatin Tarayya, ASUU, da duk masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da su kawo karshen yajin aikin da ke ci gaba da yi tare da gaggawar ceto wannan fanni daga durkushewa baki daya. Daukar natakin gaggawa zai yi tasiri sosai a fannin ilimi da haɓaka samun ingantaccen koyo. A bar shugabannin kasar nan na gobe gaba su koma makaranta.”
Bob-Manuel ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi addu’a, kuma su zabi shugabannin na gari a babban zabe mai zuwa.
A WANI LABARIN KUMA: Gwamnan Legas Ya Maye Gurbin Kwanishinan Da Yayi Murabus
Gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da tsohon kwamishinan ayyuka na musamman da hulda da gwamnatocin tarayya, Tayo Bamgbose-Martins, a matsayin sabon kwamishinan tsare-tsare da raya birane na jihar.
Kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar Mista Gbenga Omotoso ne ya sanar da hakan a ranar Laraba a Alausa, Ikeja.